Somaliya: Sojoji Sun yantar da wani yanki da ke hannun al-shabab.


 

An kori al-shabab daga wani yanki da ke hannunsu.

Kamfanin Dillacin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya ambato wani jami’in soja, na kasar Somaliya, Abdullahi, yana cewa; Sojojin kasar tare da taimakon dakarun Afirka, Amison, sun kwace iko da wani yanki da ke hannun al-shabab.

Kungiyar ta al-shabab ta fice daga yankin da ke kudancin kasar.

Sojojin kasar ta Somaliya tare da dakarun tabbatar da zaman lafiya na Afirka, suna kokarin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben da za a yi a kasar.

Sai dai kungiyar ta al-shabab ta sha alwashin tarwatsa zaben.

A halin yanzu ana gudanar da zaben yan majalisa a duk fadin kasar.

You may also like