Sony Ya Sauya Sunansa Zuwa Muhammad Sani Bayan Ya Amshi Musulunci


A ci gaba da Tafsirin da babban Malaminmu yake gabatarwa, a daren jiya Alhamis bayan mun kammala Tafsirin yamma, wanda Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ya saba gabatarwa, Allah Ya albarkaci Tafsirin da musuluntar wani dan uwa
mai suna Sony, wanda yanzu ya koma Muhammad Sani.

Allah ya karawa Malam kwarin gwiwa, imani da lafiya, ya kuma amfanar da mu darussan da muke sauraro, ya
kuma gafarta mana zunubanmu cikin wannan wata mai alfarma.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like