
Asalin hoton, Getty Images
Southampton ta kori kociyanta, Nathan Jones, bayan wata uku da ya ja ragamar kungiyar da ke buga Premier League.
Tsohon wanda ya horar da Luton Town, mai shekara 49 ya bar Southamton tana ta karshen teburi, bayan da Wolves ta doke su ranar Asabar a Premier.
Jones, ya yi rashin nasara a wasa tara daga 14 da ya ja ragama a dukkan fafatawa, bayan da ya karbi aikin ranar 10 ga watan Nuwamba.
Cikin doke kungiyar da aka yi har da rashin nasara tara a Premier League da shan kashi karo hudu a jere a St Mary.
Haka shima koci da ya taimaka masa aiki Chris Cohen da Alan Sheehan sun bar Southampton.
Ruben Selles ne zai ja ragamar kungiyar a gasar Premier League da za su ziyarci Chelsea ranar Asabar.
Jones ya maye gurbin Ralph Hassenhuttl cikin watan Nuwamba kan kwantiragin kaka uku da rabi, bayan da ya bar Luton mai buga Championship.
Kociyan ya sha kashi a wasa hudu daga biyar da ya fara jan ragama Southampton, wanda ya ci Lincon mai buga League One 2-1 a Carabao Cup.
Daga nan ya doke Crystal Palace a FA Cup da fitar da Manchester City daga Carabao Cup ya kuma doke Everton a Premier daga nan abubuwa suka bal-balce masa.
Jones ya yi suna ne a Luton a karo biyu da ya horar da ita tamaula.