SSS sun kama masu garkuwa da mutane a Kano


Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya SSS sun samu nasarar ceto wani yaro dan shekara 11 da wasu mutane suka yi garkuwa da shi tsawon kwanaki 11.

A cewar daraktan hukumar na jihar Kano, Alhassan Muhammad ofishin hukumar ya karbi takardar korafi daga wani lauya wacce tayi bayani dalla-dalla kan yadda aka yi garkuwa da yaron a ranar 8 ga watan Disamba.

An rawaito cewa iyalan yaron sun biya diyar ₦200,000 ga masu garkuwar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Shugaban hukumar ya ce masu garkuwar suna zaune ne a unguwa daya da yaron, tun farko dai sun nemi a biya su diyar miliyan ₦20 kafin daga bisani su rage kuɗin zuwa ₦200,000.

Jami’an hukumar sun gano wani bangare na kuɗin, bindigar wasa, da kuma fuska.

Mutane ukun da ake zargi sun haɗa da wani dalibi a makarantar sakandare Abba Tijjani mai shekaru 17, Jamilu Alhassan wanda yace shi dalibi ne a jami’ar Bayero da kuma Umar Salisu, dukkaninsu sun amince da aikata laifin da ake zarginsu da shi.

A cewar Salisu wanda shine ke jagorancinsu, sun yanke shawarar aikata haka ne bayan yawan kallo fina-finan kasashen waje da suke yi.

You may also like