Stella Odua ta amsa tambayoyi a hannun EFCC


Stella Odua tsohuwar ministan sufurin jiragen sama ta fuskanci tambayoyi daga jami’an Hukumar Yaƙi Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta EFCC.

Jaridar  The Cable ta gano cewa Odua ta isa harabar EFCC da ƙarfe 11 na safe domin amsa goron gayyatar da hukumar ta miƙa mata.

Odua wacce sanata ce a yanzu dake wakiltar mazabar Anambra ta arewa ta shafe wunin ranar Litinin tana amsa tambayoyi a ofishin hukumar.

Wata majiya dake ofishin hukumar ta ce an gayyaci Odua saboda ana zarginta da halarta kuɗaɗen haram da kuma zambar kuɗi har biliyan ₦ 9.4 a wata kwangilar da ta bayar ta saka kayayyakin samar da tsaro a filayen jiragen sama dake kasarnan.

Tun farkon wannan watan ne Odua ta fitar da wata sanarwa inda take musalta zargin da ake mata na karkatar da kuɗaɗen gwamnati a lokacin da take riƙe da mukamin minista.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like