Sudan:Anci Zarafin Mata a Sudan Ta kudu


U

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bada umarnin aiwatar da bincike kan matakin da dakarunsu suka dauka, yayin wani hari da aka kai a wani otel na birnin Juba.Ban Ki-Moon ya nuna bacin ransa lokacin da akagabatar masa da rahoto na karshe kan abubuwan da suka wakana a ranar 11 ga watan Yuli da ya gabata a wannan Otel, inda wasu mutane sanye da kayan soja suka kashe wani dan jarida, sannansuna yi wa mata da dama fyade a lokacin barkewar sabon fada tsakanin sojojin da ke goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da na mataimakinsa na wannan lokaci Riek Machar, inda ake zargin cewa dakarun kiyaye zaman lafiyana Majalisar Dinkin Duniya, basu yi komai ba domin hana afkuwar lamari da ma wasu jerin cin zarafin mata da aka fuskanta a birnin na Juba.

You may also like