Sudan Ta Kudu: ‘Mun yi tattakin kwana tara domin mu ga Fafaroma’



B
Bayanan hoto,

Masu ziyarar suna cike da farin ciki na irin tarbar da aka yi musu

Wata ƙungiyar kiristoci mabiya ɗariƙar Katolika masu ziyara sun yi tafiyar kwana tara a ƙafa ta cikin yankin da ake yaƙi a Sudan Ta Kudu domin su yi ido biyu da Fafaroma Francis a babban birnin ƙasar Juba.

“Ƙafafuna sun riƙa min zugi, amma fa ban ji wata gajiya ba. Lokacin da yaƙini ya ratsa ka, ba zaka taɓa ganin wuyar da take cikin abun ba,” in ji wata da ake kira NightRose Falea, wadda leɓenta ya bushe.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like