Sumamen Da DSS Ta Kai Kasuwannin Canji Ya Gaza Kara Farashin Naira


 

 

Da alama sumamen da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kai kasuwar canjin kudade a wasu sassa na kasar nan dai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Hukumar ta kai wa ‘yan kasuwar canjin farmaki ne, inda ta yi awan gaba da wasu daga cikinsu, a bisa laifin taimakawa naira faduwa da ta ce ‘yan canjin na yi.

Gwamnatin Nijeriya ita ta umarci jami’an ‘yan sandan farin kaya na DSS da su yi wa ‘yan canji dirar mikiya, sannan su kama duk wanda ke bayarda canji ba akan farashin da aka kayyade ba, da nufin dakile faduwar da Naira din ke yi.

Sai da izuwa yanzu, babu alamun cewa farashin naira na shirin karuwa, sai dai ma raguwa da yake kara yi.

Wasu na ganin hakan ta faru ne a sakamakon tsoro da ya shiga zukatan ‘yan kasuwan canjin, al’amarin da ya sa wasu daga cikinsu suka kauracewa kasuwar. Hakan kuma ya kara rage adadin kudaden kasar wajen da ake samu, a sakamako haka, farashin naira ya kara samun nakasu.

Sai dai duk da haka wasu na ganin ya na da kyua a sanya idanu a kasuwar, saboda ta na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa.

A wata hira da kafar yada labarai ta Muryar Amurka ta yi da wani masanin tattalin arzikin Malam Aliyu, ya bayyana cewa ai matsalar ta samo asali ne daga babban bankin kasa. A fadarsa, kudaden babban bankin bai kamata su shiga kasuwar canji ba.

Ya kara da cewa, ita kasuwar ta mutanen da ke shigowa kasar ne su canza kudadensu amma sai ta rikide ta zama inda hatta masu neman kudin kasuwanci da biyawa ‘ya’yansu kudin makaranta kasuwar suke zuwa.

Toh da alama dai game da matsalar faduwar farashin Naira a Nijeriya, gwamnati na zaton wuta a makera, ta na can ta na ci a masaka.

You may also like