
Rayane Souza ta ƙaurace wa hawa manyan motocin safa na birnin tsawon shekaru a yunƙurinta na tafiya ƙetare
“Abin al’ajabi ne” duk da cewar wurin a kusa da gidanmu yake, bai fi shekara biyar kenan ba na ci gaba da zuwa bakin teku domin hutawa.”
Rayane Souza ta taso ne a wani Tsibirin na Vitória, a jihar Espírito Santo da ke babban birnin Brazil.
Iyayenta sun mallaki gida a Ilha do Boi, ɗaya daga cikin wurare da ke ƙara fito da ƙayatattun wurare a birnin.
Mun haɗu a gaɓar teku, don tattaunawa kan tsangwamar masu ƙiba, wani abu da ke nuna tsangwama ga mutane masu ƙiba wadda a wani lokacin ake kira “fatpobia” da Ingilishi.
Wayar da kai kan mene ne tsangwamar masu ƙiba?
Ta kasance daya daga cikin wadan da suka kafa kungiyar dokar kare masu ƙiba wato “Gardon a Lei”, wadda ke wayar da kai game da manufar, kuma ta ƙunshi lauyoyi da wasu da suka taɓa fuskantar tsangwamar, kuma suke neman hakkinsu a kotu.
Brazil ta yi suna kan wuraren shaƙatawa na bakin teku, amma kuma ƙasa ce wadda masu raji ke nema a samar ko a amince da dokar da za ta mayar da birane inda za a rinƙa bai wa mutane masu yanayin jiki daban-daban dama.
Haka kuma lauyoyi na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun shigar da ƙararraki da ke da alaƙa da tsangwama gaban kotu, musamman a wuraren aiki, da mata da ke bukin gasar sarauyinar kyau.
A yayin da Rayane ke magana da BBC a kan wani benci da ke kallon teku, saurayinta ne ke daukar hotuna.
Za a saka hotunan ne a shafinta na sada zumunta da ke manhajar Instagram, inda ‘yar gwagwarmayar ke yaɗa abubuwa da ke faruwa a rayuwarta da mabiyanta sama da 18, 000.
Ita ce nan lokacin da take da shekaru 32 a duniya, shekaru masu yawa, a lokacin tana da yarinya mai shekara 11, da ba ta taɓa zuwa gaɓar teku ba.
Ta ce “a lokacin da nake budurwa, nakan bayar da uzuri da littafi, domin samun damar tafiya gabar teku da ƙawayena.
Nakan ce ina al’ada, ko ba ni da lafiya…. in hakan bai yi aiki ba, ni kaɗai za ka gani sanye da baƙin wando mai kama jiki, da sakakiyar riga zaune a ƙasa.”
“Na kasance mai ƙiba tsawon rayuwata. Mai ƙiba ce ni tun ina yarinya, mai ƙiba ina budurwa. Na jima ina jin maganganu kan girman da nake da shi.
Amma ta ce abubuwa sun sauya a lokacin da take jami’a.
Shiga yanayin damuwa
A 2012 , wasu ‘yan ajin su Rayane suka samar da wani dandali a manhajar Whatsapp, da ke yawan magana kan tsarin hallitar jikinta.
Sukan dauko hotonta daga kafafen sada zumunta su yi ta aibata halittarta. Sai da ta kai ɗaya daga cikin yaran ta ga cewa abin da suke yi bai dace ba, sannan ta sahidsa mata abin da ke faruwa.
To amma damuwar da ta fuskanta a wannan lokaci ne ya sauya tunaninta.
A ƙoƙarin neman hanyar samun mafita ne ta gano shirin body positive movement, wani tsari a Amurka a shekarun 1970, wanda ke koyar da yadda mutum zai kula da kuma ƙaunatar kansa.
“Lokacin da na gane mene ne tsangwamar masu ƙiba, sai na fahimci abubuwa da dama da suka faru a rayuwata. Ba laifina ba ne, laifin al’ummar da nake ciki ne.”
A shekara ta 2019, ta buƙaci wata ƙawarta mai hanƙoron kare hakkin bil’adama ta kafa wata ƙungiyar wayar da kai.
Sukan samu saƙonni kimanin 70 a kowane wata daga masu neman sauyawa ko kuma suke son bayyana labarin abin da ya faru da su.
Tsangwama a wurin aiki
Tsangwamar masu ƙiba ba laifi ba ne a hukumance a Brazil, amma akwai hanyoyin da da za a iya tuhumar mai yin irin haka a kotu, kamar shigar da mutum ƙara bisa zargin ɓata suna, ko cin zarafi, in ji Mariana.
Ta labarin wani shugaban ma’aikata wanda ya sanya dokar cewa ba zai biya ɗaya daga cikin ma’aikatansa alawus ba sai ta rage ƙiba.
‘Har sai da ya auna nauyinta a sikeli.
Alƙalai sun bai wa ƴar aikin gaskiya sannan suka yanke hukuncin biyan ta diyyar dala 1,800 – ɗaya daga cikin diyya mafi yawa da aka taɓa yankewa a Brazil kan laifin tsangwamar masu ƙiba, sai dai ba wani abin a zo a gani ba ne idan aka kwatanta da wasu diyyoyin da ake yankewa kan wasu laifukan.
Amincewa da ƙudurin, hana tsangwamar masu ƙiba
Asalin hoton, OTHER
A bara ne aka amince da dokokin haramta tsangwamar masu zanga-zanga guda biyu: ɗaya daga cikin dokar ita ce ta ware ranar wayar da kai kan tsangwamar, da kuma wadda ta tilasta wa makarantu sanya manyan kujeru a azuzuwa.
Wadda ta gabatar da ƙudurin, Cida Pedrosa ta ce “na ji labarin yadda wasu suka rinƙa fuskantar wulaƙanci a lokacin da suke makaranta, wasu sai sun je asibitin shugaban makaranta domin nemo kujera mai girma da za ta ishe su zama.