Super Eagle ba ta shiryawa gasar cin Kofin Duniya ba -Rohr


Kwanaki kadan kafin fara gasar cin Kofin Duniya na shekarar 2018 a kasar Russia,kocin kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagle, Gernot Rohr, ya ce tawagar yan kwallonsa basu shiryawa gasar ba.

Ƙungiyar ta Super Eagle ta yi rashin nasara a wasan da ta buga na karshe da kasar Jamhuriyyar Czech a shirye-shirye da take na tunkarar gasar.

Da yake mayar da martani kan rashin nasarar, Rohr ya ce rashin nasara da ci 1:0 ba abun damuwa bane a yanzu amma kuma ya bayyana bakin cikinsa kan sakamakon.

Ya ce “muna da kwanaki 9 domin shiri kafin buga wasan mu na farko da kasar Crotia ya zuwa ranar yau bamu shirya ba, bana cikin bakin ciki sanadiyyar wannan sakamakon sakamako mafi muhimmanci shi ne a kasar Russia.”

Ƙungiyar ta Super Eagle dake rukunin D za ta fara wasanta na farko da kasar Crotia a ranar 16 ga watan Yuni kafin su kara da kasashen Iceland da Argentina.

You may also like