Super Eagles ta je ta ci Guinea Bissau ta dauki fansa



Super Eagles

Asalin hoton, Super Eagles

Tawagar Najeriya ta je ta doke ta Guinea Bissau da ci 1-0 a wasa na hudu a rukunin farko da suka kara ranar Litinin a Bissau.

Sun buga wasan a Estadio 24 de Setembro, domin neman gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024.

Najeriya ce ta fara cin kwallo ta hannun Moses Simon a bugun fenariti a minti na 30 da take leda.

Ranar Juma’a Guinea Bissau ta doke Super Eagles da cin 1-0 a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, Najeriya.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like