
Likitoci su na kula da marasa lafiya a waje duk da sanyi da ake yi
Asibitoci a birnin Aleppo da ke Siriya sun cika maƙil har babu wajen kwantar da sabbin mutanen da ake kawowa da suka jikkata a girgizar ƙasa da ta afku, inda yanzu ake kokarin sallamar waɗanda aka yi wa magani, kamar aydda wani likita ya shaida wa BBC.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mutanen da suka jikkata a girgizar ƙasar da ta afku a ranar Lahadi sun a arewa maso yammacin Syria ya kai mutum 7,600, inda 4,300 suka rasu.
Gadajen kwantar da mutane a asibitin Al-Razi da ke birnin Aleppo sun yi yawan da ba za a iya saka su cikin asibitin ba.
Akwai gadaje a kowane kusurwar asibitin da ke fama da ƙarancin magunguna.
Gwamnatin Syria ta bai wa BBC damar ziyartar yankin da girgizar ƙasar ta lalata, inda kuma ta tattauna da ma’aikatan lafiya a wurin.
Dakta Nizar Suleiman da abokan aikinsa sun aiwatar da wani tsari cikin sauri don kula da duk wadanda suka jikkata
“Bamu samu damar sallamar mutane ba daga asibiti duk da na musu magani, an lalata birnin kuma babu wurin da za su je’’ in ji Dakta Nizar Suleiman, shugaban likitan kashi a asibitin Al-Razi.
“Marasa lafiya da dama sun zo asibitin cikin ƙankanin lokaci. Bamu da isassun magunguna, abin damuwa ne. Alal misali, muna fama da ƙarancin ababe na jinyar waɗanda suka samu ƙaraya. Ƙarancin magungunan ya shafe mu saboda wannan lamari da ya auku da takunkumai,’’ in ji shi.
Gwamnatin Syria ta ce takunkuman ƙasashen yamma a kan ta dangane da yaƙi ya janyo tsaiko a kawo kayan agaji.
Sai dai Amurka da wasu ƙasashe masu ƙarfin mulki sun musanta hakan, inda suka ce babu takunkumi kan bayar da kayan agaji.
Duk da cewa ba a saka takunkumi kan bayar da agajin kayan lafiya ba, ba, dokokin Amurka sun sanya wahala a buƙatar cire kuɗi, wanda zai yi tasiri mara kyau ga samar da magani daga waje.
Gadajen marasa lafiya a asibitin Al-Razi sun yi cunkoson jama’a a waje
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Syria SANA, ya bayar da rahoton a ranar Litinin cewa ministan harkokin wajen kasar Faisal al-Mikdad ya yi kira da a dage dukkan matakan tilastawa bangarorin biyu a ganawar da ya yi da wakili na musamman na MDD a Syria, Geir Pedersen.
Rasha da Iran sun ba da taimako ga waɗannan yankunan da gwamnatin Siriya ke iko da su da kungiyar Hizbullah da kuma kungiyar masu fafutuka da ke samun goyon bayan Iran a Lebanon.
Tuni dai agajin da ƙasashen China da Sudan da Aljeriya da Iraki da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa suka bayar ya isa ƙasar kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta Syria ta bayyana.
BBC ta ga tallafin da Rasha ke bayarwa ta manyan motoci zuwa wata cibiya a wata coci da suka haɗa da barguna da kayan agajin jin kai.
Lamarin dai na da wuya, amma asibitin na tsaye da kafafunta. “Gwamnati da wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun taimaka mana wajen shawo kan matsalar ƙarancin magunguna.” Inji Dakta Suleiman. “Amma akwai ƙarancin magunguna, musamman magungunan kashe radaɗi da kuma na ƙarfafa garkuwar jiki”
Asibitoci na fama da yanda za su karɓi tare da kwantar da sabbin marasa lafiya
Baya ga yankunan da ‘yan adawa ke rike da su a Syria, al’ummomin da ke yankunan da gwamnati ke iko da su, sun san cewa ƙarin taimakon agaji na zuwa nan ba da daɗewa ba.
A ranar Asabar makwabtan Siriyan, Lebanon, ta bayyana cewa za ta buɗe tashoshin jiragen ruwa da na sama don bai wa ƙasashen da suke son aika taimakon agaji damar yi ta ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labaran Iran FARS ya ruwaito cewa jiragen ruwa ɗauke da kayan agaji sun isa, wanda kuma ya kunshi barguna da tantuna da magunguna da kuma abinci.
Ana ganin kayan agajin zai tsaya ne kawai a yankunan da gwamnati ke iko da su.
Ministan harkokin wajen ƙasar ta Syria, Faisal al-Mikdad, ya ce yana ƙoƙarin ganin an kai kayan agaji ga dukkan waɗanda suke buƙata a kuma dukkan yankuna, ba tare da nuna bambanci ba.
Sai dai, kungiyoyin ‘yan adawa da ke rike da ikon wasu yankuna, basa karɓar agaji daga wajen gwamnati, inda suka fargabar cewa gwamnatin ƙasar za ta ayyana samun nasara.
Ɓarnar da aka yi wa birnin Aleppo dai na ƙara munana.
Yayin da suke tafiya ta cikin birnin, tawagar BBC ta yi ƙoƙarin yin tsit ko watakila za su ji muryoyin waɗanda suka tsira daga ɓaraguzan gine-gine.
Mako ɗaya bayan afkuwar girgizar ƙasar, yanzu dai damar samun waɗanda suka tsira na raguwa.
Sai dai, waa ci gaba da kawo waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci, inda al’amura kuma ke ƙara kamari saboda yawan mutanen da abin ya rutsa da su.
Abu Muhammad ke nuna hoton iyalansa
Abu Muhammad yana cikin waɗanda suka tsira, bayan shafe kusan sa’o’i 24 a karkashin ɓaraguzan ginin.
Shi ne mahaifin ‘ya’ya biyar, ya rasa matarsa da uku daga cikinsu a girgizar kasar. Yana kallon hoto kala-kala a wayarsa na iyalansa a lokutan farin ciki.
“Na rasa matata da ‘ya’yana,” ya faɗa yana kuka. Ya yi godiya ga abu ɗaya: “Allah ya kare min wayata don tunawa da su domin in rika kallon hotunansu duk lokacin da na ji kewarsu.”
“Har yanzu na kasa yarda da abin da ya faru da ni, wani lokacin ina ji kamar mafarki ne, mummunan mafarki, ba zai iya zama gaskiya ba.”
Mutanen da girgizar ƙasa ta shafa suna rayuwa yanzu a cikin majami’u da masallatai ko a wuraren taron jama’a da wuraren shakatawa bayan sun rasa gidajensu.
Mutane sun shaida mana cewa a lokacin yaƙin basasar ƙasar da aka kwashe sama da shekaru goma ana yi, kusan sun yi tsammanin za su iya rasa ‘yan uwa ko dukiyoyinsu.
Amma girgizar ƙasar ta kasance ba zato ba tsammani. Ta afku lokacin da mutane suke barci, inda haka ya kawo wahalhalu ga mutane wanda kuma suke ganin na da wuyar jurewa.