Syria-Mutane suna komawa birnin Manbij


 

 

Dubunnan mutane ne suka koma gidajensu a birnin Manbij na Syria, bayan tserewar mayakan IS daga birnin.

 

Wannan kome ya biyo bayan sanarwar ‘yan tawayen Syria da ke samun goyon bayan Amurka na kwace birnin daga mayakan na IS.

Rahotanni sun ce anga daruruwan motoci dauke da mutane daga sansanonin wucin gadi suna komawa cikin birnin, bayan tserewar da suka yi lokacin da mayakan IS suka mamaye yankin a baya.

You may also like