Syria: Yawan mutanen da suka mutu a harin Aleppo ya karu


2016-09-05t123357z_1172366295_s1aetznysjaa_rtrmadp_3_mideast-crisis-syria-aleppo

 

Rahotanni daga Syria sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da jiragen yakin Rasha suka kai, a yankunan Idlib da Aleppo, da suke karkashin ikon ‘yan tawayen Syria, ya karu daga 80 zuwa 100.

An dai kai harin sa’o’i kalilan bayan Rasha da Amurka sun sanar da cimma matsayar kawo karshen fadan da aka kwashe shekaru biyar ana yi a Syria.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da Ministan harkokin waje na Rasha, Sergei Lavrov sun ce yarjejeniyar da aka cimma a Geneva a ranar Juma’a zata fara aiki ranar Sallah Babba, wato gobe Litinin.

Ana sa ran idan har wannan yarjejeniya tayi nasara, akwai yiwuwar Rasha da Amurka su hada gwiwa don murkushe mayakan ISIL.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like