Syriya da Rasha sun fara kai kayan agaji a Aleppo


 

Wani bangare na mutanen Alepo ne kawai suka amfana da sabon ayarin agajin jinkai da gwamnatin kasar Syriya da aminiyarta Rasha suka tsara a birnin, kamar yadda kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar (OSDH) ta sanar.

Kirkiro wannan ayarin jinkai dake kasancewa wani yinkurin tausayawa fararen hula da gwamnatin Bachar el-Assad da abukiyar kawancenta Rasha, suka tsara na zama wani tarko ne da aka hakawa yan adawar kasar a cewarsu.

A bangaren MDD wannan ayarin na kai kayyakin taimakon jinkai abin yabawa ne, sai dai bai wadatarba wajen tunkarar dimbin bukatar da ake da ita domin magance matsalar jinkai da ake fama da ita a wasu unguwanin dake rike ga hannun yan tawayen a birnin Alepo

Ministan tsaron Rasha, Sergei Shoigu, yace an bude hanyoyin fita uku dan baiwa mutanen da akayi garkuwa da su damar sakin mara da kuma mayakan dake bukatar aje makaman su.

Akalla mutane 250,000 ke zama a birnin na Aleppo.

You may also like