Ta Ƙona Mijinta Da Tafasasshen Ruwa A Legas


Wata mata da ake kira da suna Joy ta ranta a na kare bayan da ta watsawa mijinta Akachi tafasasshen ruwan zafi saboda haushin ya ki bude mata kofa ta shiga gida, yayin da ta koma a makare misalin karfe goma sha daya na dare.

Ma’auratan na zaune ne a yankin Iyani Itire da ke Oshodi a cikin garin Legas.

Rahotanni sun ce mijin matar ya ki yarda ya bude mata kofa ne, saboda tuhumar da yake mata na bai yarda da inda ta je har ta kai dare ba. Sai da gari ya waye ta shiga gidan ta tafasa ruwa, kamar za ta shiryawa yara abin karin kumallo sai kawai ta juye a jikin mijinta, Akachi.

Yanzu haka dai Joy ta tsere, yayin da ‘yan sanda ke cigiyar inda ta gudu ta buya.

You may also like