Ta Kashe Mijin Ta Da Maganin Ɓera A Kano


A yau Talata, wata kotun Majistare da ke Kano ta bada umarnin tsare wata matar aure ‘yar shekara 16 a gidan tsaron yara masu laifi, sakamakon zarginta da ake na kashe mijinta da guba.

Ana tuhumar matar, wacce ke zaune a kauyen Shitta da ke Karamar Hukumar Danbatta, Jihar Kano, da laifin aikata laifin kisan kai.

An zarge ta da laifin kashe mijinta mai suna Auwalu Isah da guba.

Mai shari’ar Kotun Majistare din, Hajiya Fatima Adamu, wacce ta bada umarnin tsare mai laifin, ta jinkirta karar har zuwa 7 ga watan Yuni.

Wanda ya gurfanar da mai laifin, Insifekta Aluta Mijinyawa, ya sanar da kotun cewar wani mutum mai suna Ibrahim Yahaya ne ya kai rahoton kisan kan ga ofishin ‘yan sandan Danbatta, ranar 25 ga watan Afrilu.

Ya ce ran 22 ga watan Afrilu, misalin karfe 7 na dare, wacce ake zargin ta dafa wa mijinta Isa, dan shekara 35 abinci, sannan ta gauraya abincin da maganin bera.

“Bayan mijin nata ya ci abincin, sai ya mutu nan-take sakamakon guba da ke cikin abincin,” inji shi.

Bayan haka, wacce ake zargin ta karyata zargin da ake mata.

A dangane da bayanin mai karar, laifin ya saba wa sashi na 221 na kundin Final Kod.

You may also like