Ta Nemi Mijinta Ya Sake Ta Saboda Ya Fifita Soyayyarta Fiye Da Ta Mahaifiyar SaWani dan kasar Saudiya mai suna Baha mai shekaru 29 ya tsinci kansa a kotu, inda matarsa ta kai kararsa domin ya sake ta saboda ya fifita son da yake yi mata fiye da ta mahaifiyarsa. 

Majiyarmu ta Saudi Gazetti, ta rawaito cewa Mijin ya yi matukar kidimewa bisa karar ta sa da matarsa ta yi, domin a tunaninsa babu abinda ba ya yi mata game da ababen more rayuwa da kuma sauran al’amuran da suka jibanci mu’amalar aure.

” Ba zan taba amincewa da mijin da yake nunawa matarsa soyayya, yayin da kuma bai damu da mahaifiyarsa ba”, kamar yadda matar ta bayyanawa Alkalin kotun. 

Ta ce mijinta yakan kashe mata kudi sosai har ya fita da ita yawon shakawata zuwa kasashen waje tare da saya mata duk wani abu da take bukata, amma ta ce ba ta bukatar ci gaba da zama da shi saboda bai damu da mahaifiyarsa ba.

Ta ce “duk mutumin da ba ya kyautatawa mahaifiyarsa, babu shakka wata rana zai iya juyawa matarsa baya”. 
Ta ce dukkanin hujjojin da mijin nata ya gabatar a kotun game da kyautatawar da yake yi mata gaskiya ne, amma kawai tana bukatar ya sake ta ne saboda ya juyawa ‘yan uwansa baya ciki har da mahaifiyarsa saboda kawai soyayyar da yake yi mata a matsayin matarsa.

You may also like