Tun bayan Maryam ta soka mijinta Bilyaminu wuka wanda hakan ya zama sanadiyyar rasuwar sa. Hakan ya zama tamkar ba wa Mata lasisin Sokawa Mazajen su. A unguwar ‘Yandodo da ke Hotoro a karamar hukumar Nassarawa, Hadiza ta Sokawa mijinta Balarabe wuka saboda yana gina sabon gida. Wanda a zargin ta wai Aure ya ke nufin karawa.
A halin yanzu ya na asibitin Marigayi Malam Aminu Kano, sakamakon raunin da ta yi masa.