Ana bayyana ta da wacce ta lashe gasar Karatun Al-‘Kur’ani mai girma ta kasa sai Hafiza Amina Ahmad daga Barno, ta sunkuya kasa tana mai yi wa Allah sujjada don gode masa.
An kuma ba ta kyaututtuka kamar haka:
1- Kujerar aikin hajji.
2-Tsuleliya, sabuwa, kuma kyakkyawar mota.
3-Tsabar kudi Naira 500,000.
4-Sabuwa kuma dan’kareriyar wayar Laptop.
5-Kur’aani mai rubutu mai motsi (digital Kur’an).
6-Dardumar Sallah mai kyan gaske.
Allah Ya sa albarka kuma ya kara mata tsoronSa.