Tabar WiWi Ka Iya Kawo MAKANTA – KwararruWasu kwararru a kasar Faransa sun yi gargadin cewa mutane suka jima suna  ta’ammali da tabar Wiwi za su iya makancewa.
Bayanin wanda aka wallafa a cikin mujallar kungiyar likitoci na Amurka ya nuna cewa yawan amfani da wiwi yana raunana sinadiran kwayar ido da kuma jijiyon da ke rike da shi. 

Binciken ya gano cewa mutanen da suka kwashe shekaru shida suna shan wiwi suna samun jinkiri wajen isar da sako daga Ido zuwa ga kwakwalwa wadda ita ce ke fassara abin da ido ya hango.

You may also like