An tabbatar da Trump a matsayin Shugaban kasar Amurka na 45.


 

 

Wakilai A Amurka sun Kada Kuri’ar Tabbatar Da Donald Trump a matsayin zababben Shugaban kasar na 45.

A Daren jiya Litinin ne Wakilai 270 na Amurka sun kada kuri’ar tabbatar da zaben da aka yi wa hamshakin mai kudin nan, sananne a harkar gine-ginen gidaje, Donalp Trump a matsayin  shugaban Amurka na 45, duk kuwa da cewa wasu ‘yan kasar sun yi ta gudanar da zanga-zanga na neman wakilan kadda su amince da su.

Tun a farkon watan Nuwamba sun san cewa Donald Trump shine zai karbi ragamar mulkin Amurka bayan an rantsar dashi a ranar 20 ga watan Janairu mai zuwa.Sai dai kuma zaben Amurka ba ya kammala da zaben gama gari, sai bayan da wakilai suka kada kuri’ar amincewa da wannan ya lashe zaben

A bisa tsari wanda yafi samun kuri’u mafi rinjaye a akowace jaha shine ke samun daukacin wakilai, wanda ake bayar da yawan kuri’unsu kwatankwacin yawan jama’ar da suka jefa kuriar su a wannan jahar.

‘Yar takarar jamiyyar Democrat, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta zarta Trump da kuri’u miliyan 2.9 a zaben kasa baki daya. To amma sai dai Trump din ya fita samun nasara a jihohin da suka fi tasiri.Domin kuwa ya samu wadatattun kuri’u har 306 sama da 270 da ake bukatar ya samu na wakilai.

You may also like