Taiwan da Chaina rikici na ta’azzara | Labarai | DWChaina ta ce ta gwada kaddamar da wasu jerin hare-hare a muhimman abube na tekun Taiwan, a ci gaba da atisayen sojin da take a rana ta biyu kusa da tsibirin, duk da kakkausar sukar da ta ke sha daga wasu manyan kasashen yamma ciki har da Amirka.

Sabon atisayen mai suna “Joint Sword” na a matsayin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro ne da Bejin ke yi, a wani mataki na mayar da martani kan ziyarar shugabar yankin Taiwan a Amirka.

Tuni ma dai ma’aikatar tsaron Taiwan ta tabbatar da ganin dandazon jiragen ruwa na yakin Chaina 9 da 58, kana Taipei ta ce ta fargar da dakarunta da su kasance cikin shirin ko ta kwana.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like