
Asalin hoton, PDP
Cacar baki ta kaure tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da ta PDP mai hamayya a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne bayan da jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa gwamnatin Katsina ta hana ta amfani da filin wasa na Muhammad Dikko da za ta yi gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasarta da na gwamnan jihar da sauran ‘yan takara.
Shugaban kwamitin yakin neman zaben na dan takarar shugabancin Najeriya na PDP a Katsina, Sanata Ibrahim Tsauri, ya ce sun shirya gudanar da taron dan takararsu na PDP, Atiku Abubakar da na gwamnan jihar Sanata Yakubu Lado Dan marke da na sauran ‘yan takararsu a ranar 20 ga Disambar nan a filin kwallon.
Sanata Tsauri ya yi zargin cewar gwamnatin Jihar ta Katsina ta hana su yin amfani da filin tana mai ikirarin cewa ana gudanar da gyara a cikinsa.
Ta ce sai dai su yi amfani da filin wasa na polo domin gudanar da gangaminsu na yakin neman zabe.
Sai dai ya ce babu wani gyara da ake yi a filin wasan na Muhammad Dikko.
Sanata Ibrahim Umar Tsaurin ya ce “sati hudu da suka gabata mun rubuta musu takarda, sai suka rubuto amsa cewa ba za su bayar da filin ba sai dai mu yi amfani da filin wasa na cikin gari. Mun san matsalar da amfani da filin cikin gari zai haifar wa mutanen Katsina musamman marasa lafiya da ke babban asibitin da gidan mahaukata, da sauran wurare, kuma ga shi ranar akwai zirga-zirgar ma’aikata.”
A wata wasika da ofishin sakataren gwamntin jihar ta Katsina ya fitar a ranar 13 ga Disambar da mu ke ciki, mai dauke da sa hannun Ibrahim Nuradden da aka rubuta wa shugaban jam’iyyar PDP na jihar, ta ce ana gyara a filin, don haka ba za ta iya amincewa da bukatar PDP na yin taro a filin wasan ba.
“An umarce ni da na ba ku amsa kan wasiƙarku ta ranar 6 ga watan Disamba, kamar yadda muka sanar da ku a wasikarku ta ranar 26 ga watan Octoban da ya gabata, har yanzu ana gayara a filin wasa na Muhammad Dikko, don haka ba za ku iya amfani da shi ba wajen taron naku ba.”
Asalin hoton, Katsina Post
Filin wasa na Muhammadu Dikko a Katsina
Sai dai a wata wasikar kuma da gwamnatin ta Katsina ta fitar a jiya jim kadan bayan koken da shugabancin kwamitin yakin neman zaben dan takarar na PDP da na gwamnan jihar a Katsina ya gabatar, gwamnatin ta ce an kammala gyaran wannan fili.
Takardar, wadda aka rubuta ta tun a ranar 16 ga Disambar nan, dauke da sa hannun Baban Sakatare da ke kula da harkokin siyasa ofishin sakataren gwamnatin jihar, Suleiman Kankia, ta ce an kammala gyaran kuma PDP za ta iya gudanar da gangamin nata a can.
Salisu Majigiri ya tabbatar da cewar shugabancin Jam’iyyarsu na PDP ya sami kwafin wasikar, wanda yanzu za su gabatar da taron nasu a filin wasa na Muhamamd Dikko sabanin Filin Polo da suka sanar a baya.
A gobe Talata ne dai ake sa rana jam’iyyar ya PDP za ta gudanar da gangamin taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar ta Atiku Abubakar da na gwamnan jihar Honorabul Yakubu Lado Dan Marke da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a matakai daban-daban da ke jihar.