Takaddamar kasashen Afirka da ICC


Shugabannin Kungiyar Tarayyar Afirka na Kigali na Ruwanda a taron da zai duba matsaloli kama daga rikicin Sudan ta Kudu da yunkurin kyautata zirga-zirga tsakanin kasashen.

A taron na shugabannin na Afirka baya ga rikicin Sudan ta Kudu, akwai kuma batun huldar nahiyar ta Afirka da kotun ICC mai hukunta manyan laifuka, wadannan su ne za su kasance gaba a jadawalin taron. Wasu kasashen Afirka dai na neman kungiyar ta AU fice baki daya daga kotun ta ICC, amma akwai masu adawa da hakan kamar kasar Botswana.

Taron kuma ya zo ne ‘yan kwananki bayan fafatawa da aka yi tsakanin sojoji da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu, abin da ya sa ake gudun kasar za ta koma wani yakin basasa. Rudanin da aka samu ya kawo shakku kan yarjejeniyar da aka kulla a watan Augusta na bara, tsakanin Shugaba Salva Kiir da jagoran ‘yan tawaye Riek Machar. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda ya halarci taron na kasashen Afirka, ya yi kira da a saka wa Juba takunkumin hana sayar musu makamai.

You may also like