Takaitattun Labarai – 11/10/2016


*Shugaba Muhammadu Buhari ya bude taron Tattalin Arziki na Kasa na 2016 a safiyar jiya, a dakin taro na otel din Transcorp Hilton a birnin tarayya Abuja.

*Taron na wannan shekara wanda zai dauki tsawo kwanaki uku ana gudanar da shi zai fi daukar hankali ne kan tallata yin amfani da kayayyakin da aka samar a Nigeria domin samun nasarar farfado da tattalin arzikin kasa da karawa naira karfi.
*Manyan masana tattalin arziki na ciki da wajen kasar nan ne za su tattauna yayin taron. A karshen taron, za a mikawa Shugaba Buhari, cikakken rahoto kan taron, wanda Shugaban ya bada tabbacin zai yi masa kyakkyawan karatu tare da yin aiki da shi.
*Shugaban Naijeriya Muhammadu BUHARI, da Mataimakinsa Yemi Osinbajo, Ministoci da masana harkar tsimi da tanaji da tattalin arzikin kasa a taron sun tabbatar ma ‘yan Najeriya cewa wannan gwamnatin ba ta barci, aiki ta ke yi Tukuru domin ganin Najeriya ta gyaru.
*Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya ce lallai mutanen Najeriya za su ga canji mai ma’ana domin abubuwan da suka sa a gaba cikin ikon Allah komai yana daidaituwa.
*Shugaba Muhammad Buhari ya kalubalanci ‘yan Nijeriya su rika amfani da kayayyakin da ake samar wa a cikin gida a wani mataki na nuna kishi da kuma taimakawa wajen samar da ayyukan yi ga matasa.
*Shugaban ya yi wannan ikirarin ne jiya a lokacin da yake bude taron koli na tattalin arzikin Nijeriya karo na 22 wanda aka yi a Abuja ya ce rungumar kayayyakin cikin gida zai taimakawa Nijeriya wajen dogaro da kanta a maimakon shigo da kayayyakin kasashen waje.
*Zuwa yanzu alkalai 7 ne ke hannun jami’an tsaron Najeriya bisa zargin cin hanci da rashawa a lamuran shari’a.
*A wani Sabon Rahoto ya nuna cewa hukumar ta DSS ta saki alkalan dukkan su guda bakwai wanda ta kama a tsakanin ranakun Juma’a da Asabar din da suka gabata. Duk da cewa an bada belinsu, amma za a ci gaba da gudanar da bincike kafin daga bisani a maka su a kotu.
*Babban alkalin Najeriya Jostis Mahmud ya nuna damuwa kan yadda a ka damke Alkalan inda ya shirya taro da hukumar shari’a don tattaunawa kan lamarin.
*An Haramta Muzaharar Addinin Shi’a  A Jihohin Kano Da Katsina. Sanarwar ta fito ne daga Jami’in hulda da jama’a na  rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Salisu Abubakar Agaisa. Wanda ya bayyana cewa duk wata kungiya ko wani da aka kama ya keta dokar zai hadu da fushin hukuma.
*Haka ma rahotanni sun nuna cewa a jihar Kano ma an sanya doka makamancin haka. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Musa Magaji Majiya ne ya bayyanawa manema labarai hakan.
*Hukumar Kwastam ta ce ta na kokarin fitowa da wata doka domin ganin an hana shigowa da shinkafa kasarnan kwata-Kwata.
Hukumar ta ce duk da har yanzu ana iya shigowa da shinkafa ta hanyar jiragen Ruwa da na sama, zuwa shekara mai zuwa za’ a hana hakan gaba daya.
*Hukumar tace gwamnati na Kashe makudan kudi domin shigowa da shinkafan saboda haka gwamnati za tayi amfani da kudin wajen tallafa wa manoman gida ne maimako kashesu akan yan kasuwa masu safaran shinkafan.
*Hukumar ta kwastam tace Kamata yayi ace za mu iya noma shinkafan da za mu ci a kasar Naijeriya


Like it? Share with your friends!

0

You may also like