Takaitattun Labarai  23/05/2017– Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Majalisar Dokokin jihar ta dakatar da binciken da ta ke yi wa masarautar Kano dangane da zargin kashe kudade ba a kan ka’ida ba.
– An gudanar da Jana’izar uwar Gidan Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a jiya Litinin wadda ta rasu bayan fama da doguwar jinya a birnin Kano. Marigayiya Shatu Aminu Kano ta rasu tana da shekaru 89 a duniya.
– An Gudanar da jana’izar wasu ‘yan gudun hijira 4 da mayakan Boko Haram suka yiwa yankan rago a Dalori da ke Jihar Barnon Najeriya.
– Ministan shari’ar Gambia, Abubacarr Tambadou ya zargi tsohon shugaban kasar da sace kudin da ya kai Dala miliyan 50 ta hannun kamfanin sadarwar kasar, yayin da kotu ta sanya takunkumi kan kadarorinsa.
– Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin samar da zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Falasdinawa. Trump ya bayyana haka a yayin ganawarsa da shugaban al’ummar Falasdinu Mahmud Abbas a yankin yamma ga kogin Jordan a yau Talata.
– Tsohuwar shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-hye ta musanta aikata ba dai dai ba a tuhumar da aka fara yi ma ta kan zargin aikata wasu laifuka da suka hada da cin hanci da rashawa.
– Hukumomin Birtaniya sun tabbatar da mutuwar mutane 22 sakamakon wani harin ta’addancin da aka kaddamar a wani wurin cashewa da ke birnin Manchester a cikin daren jiya.

You may also like