– A Najeriya, gwamnatin kasar ta baiwa ‘yan kwangila wa’adin mako biyu su kammala aikin gyaran gadar Tatabu dake jahar Nija, wacce ta hada arewa maso yammacin kasar da kuma kudancinta.
– Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tarayya ta Kano ta tsakiya a Sanata Musa Kwankwaso yana mai cewa matasan da basu da aikin yi ne ake anfani dasu wajen haddasa tashe tashen hankali.
– ‘Yan Boko Haram 52 da suka tuba suna sansanin koyas da sake hali dake Gombe inda ko a watan jiya ma an yaye wasu guda shida da suka tuba kafin wadannan na yanzu.
– Gidauniyar Dangote ta bada tallafin Naira milyan 50 ga Hausawa da Yarabawa, wadanda rikicin kabilanci ya shafa tsakanin sassan biyu ya rutsa da su a watanni baya a Sabo Ile-Ife.
– Dan shugaban Amurka Donald Trump ya amsa cewa ya gana da wata lauya ‘Yar kasar Rasha inda suka tattauna kan ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton.
– Kwanaki kadan suka rage, kamfanin Apple su fitar da sabuwar wayar su ta iPhone 8, kusan ana iya cewar jama’a sun kusan gama sanin sabon tsarin dake cikin wayar. Kamfanin dai na kokarin cika shekara 10 da kafuwa.
– Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kammala sayen tsohon dan wasantan kuma kaftin a kungiyar kwallon ta Manchester United Wayne Rooney, wanda ya bar kungiyar ta Everton zuwa Manchester a shekara 2004 kimanin shekaru 13 da suka wuce.
– James Rodriguez Na kungiyar Real Madrid ya Koma kungiyar Bayern Munich a matsayin aro na tsawon shekara biyu. Sannan Dan wasan Gaba na everton Lukaku ya kammala komawarsa Kungiyar Manchester United.
-Ambaliyar Ruwa ta yi sanadiyyar rayuka da dukiyar mutane da yawa, inda wani mutum ya rasa matansa guda biyu da ‘ya’ yansa guda shida.
-Sarkin Musulmi ya roqi matasa maza da mata da su rage hawa kafofin sadarwa na zamani irinsu Facebook, Twitter, Instagram, whatsapp da sauran su, domin hakan yana bata tarbiyarsu dakuma dabi’un su.
-Yan Sanda Sun sami nasarar cafke wani mutum da yayiwa matan aure har guda bakwai fyade.