Al’ummar garuruwan Dagumawa, ‘Yar Sarki, Danfadal da Gwari da ke cikin Karamar Hukumar Wudil sun koka kan yunkurin kwace gonakansu da aka yi domin kafa Kamfanin Solar.
Al’ummar sun bayyana wa manema labarai cewar sun wayi gari kawai da ganin wasu ma’aikata suna auna gonakan nasu, wannan tasa suka runtuma gaban dagatan wadannan garuwa domin jin ko suna da masaniya kan wannan aiki, inda suka tabbatar masu da cewar ba wanda ya tuntube su kan haka.
Da yake jawabi a madadin al’ummomin wadannan garuwa, Malam Muntari Lawan daga garin Tudun Gunsau, ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewar suna bukatar a ceci rayuwar al’ummomin wannan yanki.
Ya ce “idan wannan al’amari ya faru za mu iya barin garin nan baki daya, a halin yanzu wannan matsala za ta shafi sama da magidanta dubu da doriya, skwai auratayya a tsakaninmu wadda idan wannan abu ya faru za mu yi rabuwar da kila har abada wani ba zai kara ganin wani ba.”
Da yake mayar da martani kan zargin, shugaban Karamar Hukumar Wudiln Hon. Sale Kausani ya tabbatarwa da wakilinmu cewar wannan duk shaci-fadi ne, domin a cewarsa “Mai girma Gwamna Ganduje ne ya kira mu kananan hukumomi bakwai har da ta mai girma Gwamna Ganduje, aka bayyana mana cewar akwai wasu ayyukan ci gaban al’umma da Gwamntin Kano za ta gudanar da hadin guiwa da wasu kamfanoni domin inganta rayuwar al’ummar Kano, shi ne bayan gudanar da bincike da kwamitin da gwamnati ta kafa ya bayar da shawara kan wuraren da ake magana a kansu. Kuma Mun zauna da al’ummar wanna yanki tare da bayyana masu alfanun wannan aiki.”