
Asalin hoton, Getty Images
Kakakin majalisar dinkin duniya Stéphane Dujarric, ya ce matakin na hana mata da ke aiki da hukumomin majalisar shi ne abun damuwa na baya-bayan nan da ke yi wa hukumomin agaji tarnakin aiki a kasar wadda sama da yawan al’ummarta miliyan 40 ke bukatar taimako.
Ya ce Majalisar na kokarin kaiwa ga mutane miliyan 23 – maza da mata da kananan yara domin ba su agajin da suke matukar bukata su rayu.
Jami’in ya ce suna sa ran tattaunawa da masu mulkin na Afghanistan ‘yan Taliban domin samun cikakken bayani kan hana matan aiki.
Ya ce za su yi kokarin ci gaba da amfani da duk hanyoyin da suka kamata domin tabbatar da ganin sun kai taimakon ga wadanda suke cikin tsananin bukata musamman mata da ‘yan mata da yara.
Bayan da Taliban ta hana yawancin mata ‘yan Afghanistan aiki da kungiyoyin da ba na gwamnati ba a watan Disamba kungiyoyin agaji sun jaddada cewa wasu muhimman ayyukan kamar na lafiya, da suka hada da allurar rigakafi ba wadanda za su yi su idan ba ma’aikata mata ba.
Daga nan ‘yan Taliban din suka sassauto inda suka bar mata su yi aiki a bangaren kula da lafiya kawai.
Kafin yanzu matakin hana mata aikin bai shafi wadanda suke aiki a hukumomin majalisar dinkin duniya ba.
Tun bayan da ‘yan Taliban suka kwace mulkin kasar ta Afghanistan a watan Agusta na 2021, mahukuntan sun takaita wa mata shiga ayyuka da sauran harkoki na rayuwar jama’a, ciki har da hana su zuwa jami’o’i.
Wannan kuwa ya kasance ne duk da irin tattaunawa da aka samu aka yi da mahukuntan yan Taliban, wadanda a lokacin suka nuna alamu na sassauci da fahimtar al’amura amma daga baya kuma suka koma gidan jiya, inda a shekarar da ta gabata suka fito da dokokin hana mata zuwa manyan makarantu da aiki da kungiyoyin da ba na gwamnati ba da sauransu.