Mayakan kungiyar Taliban sun yi amfani da katuwar mota dauke da bama-bamai wajen kaddamar da farmaki a wani Otel da ke birnin Kabul, inda bakin kasashen ketare ke yawaita zama.
An dai share tsawon sa’oi bakwai ana fafatawa tsakanin jami’an tsaro da kuma kungiyar, inda rahotanni ke cewa an kashe dan sanda guda tare da raunata wasu.
Sai dai shugaban rundunar ‘yan sandan kasar, Abdul Rahman Rahimi ya shaida wa manema labarai cewa, babu wanda ya jikkata ko rasa ransa daga cikin ma’aikata da kuma bakin Otel din.
Tuni dai aka kawo karshen arangamar tsakanin jami’an tsaron da kungiyaar taTaliban.
A cikin watan jiya ne kungiyar IS mai da’awar jihadi ta kai wani kazamain farmaki a birnin na Kabul, inda ta hallaka mutane fiye da 80.