Tallafin 3,000 ga wadanda aka zarga da BH


Rundunar sojin Najeriya ta ce ta saki mutane 249 da ake zargi da alaka da kungiyar Boko Haram daga inda ake tsare da su.

Kakakin rundunar sojin kasar Kanal Sani Usman Kuka-Sheka, ya shaida wa BBC cewa an kuma bai wa ko wannensu kudi kwatankwacin dalar Amurka goma (Naira 3,000).

Rundunar ta ce ta wanke mutanen daga zargin da ake yi musu ne bayan kammala binciken da ta yi.

Sai dai ba ta bayar da cikakken bayani kan tsawon lokacin da aka yi ana tsare da su ba.

Karin bayani daga Kanal Kuka-Sheka

Bayan an wanke mutanen sai rundunar soji ta mika su ga gwamnatin jihar Borno

Mutum 169 daga cikin 249 da aka saka maza ne, 46 kuma mata yayin da 34 kuwa yara ne.

Daga cikin mutanen 203 sun fito ne daga kananan hukumomi 18 na jihar Borno, 44 kuma sun fito ne daga jihohin Adamawa da Jigawa da Yobe da Lagos da kuma Uyo.

Akwai kuma mutum biyu ‘yan kasar Kamaru da tuni su kuma aka mika su ga hukumar shige da fice ta Najeriya don mayar da su kasarsu.

An kama wadannan mutane ne a lokuta da kuma wurare daban-daban.

Zargin cin zarafi

To sai dai a lokuta da dama kungiyoyin kare hakkin bil adama suna zargin hukumomin soji da kama tare da azabtar da mutanen da babu ruwansu bisa zargin kasancewa ‘yan Boko Haram.

Amma kakakin rundunar sojin ya ce: ”zargin ba shi da tushe, bisa la’akari da irin ta’addancin da ake fama da shi a Najeriya, dole ne ya kasance za a dinga samun wadanda ake zarginsu har a kai ga tsare su.”

Ya kara da cewa ana yin bincike sannan a saki marasa laifi ba tare da cin zarafin kowa ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like