Tallafin Dala Miliyan $800M Don Cire Tallafin Mai A Najeriya Ya Janyo Cece-Kuce
Wannan dai wasu na ganin abin alheri ne, yayin da wasu kuma ke cewa hanya ce ta tsawaita bauta da Najeriya ke yi wa kasashen da suka ci gaba.

Ministar Kudi da Tsare-Tsare Zainab Shamsunah Ahmed ce ta yi bayani cewa bankin duniya ya kawo wa Najeriya dauki a daidai lokacin da ta kuduri aniyar kawo karshen tallafin man fetur, nan da watan Yuni na bana, don haka ta fara wani tsari na rage wa ‘yan kasar wahala.

Zainab ta ce bankin duniya ya bada makudan kudade da suka kai dalar Amurka miliyan 800 domin tafiyar da ayyukan jinkai, kuma an fara tunkaran gidaje kusan miliyan 10 ko kuma ‘yan Najeriya miliyan 50, masu rauni a farkon lamarin.

To sai dai ga kwararre a fannin zamantakewar dan Adam, Abubakar Aliyu Umar, yana ganin ba tallafi ne ya sa bankin duniya ya ba Najeriya kudin ba.

Abubakar ya ce bankin duniya yana bada irin wannan tallafin ta hannun dama ne kuma ya karba ta hannun hagu, saboda dole Najeriya ta biya kudin nan gaba.

Ya kara da cewa ya fi ganin shi a matsayin mahukunta na yi wa kansu tallafi ne kawai, saoda kwana nawa ya rage su bar kujerar mulki? In ba haka ba me zai sa ba za su bar cire tallafin man fetur wa gwamnati mai shigowa ba?

A nasa bangaren, Kwararre a fannin tattalin arziki na kasa da kasa, Shuaibu Idris Mikati, ya nuna alfanun wannan mataki yana cewa Babban Bankin Duniya ya ga ya kamata ya taimaki Najeriya akan kudurinta na cire rangwame a kan man fetur, shi ne ya bada gudumawa, wanda shi ba bashi ba kuma shi ba kyauta ba, wani abu ne mai garasgaras har na dalar Amurka miliyan 800, domin a tallafa wa masu rauni a kasar idan an cire tallafin man fetur a watan Yuni na wannan shekara.

Ministar Kudi Zainab Shamsunah Ahmed ta yi nuni da cewa tuni aka samu kyakyawar alaka da sabuwar Majalisar mika mulki ta Shugaban kasa da kuma gwamnati mai shigowa da nufin tafiyar da shirin kamar yadda aka tsara.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like