Shugaban Kwamitin Harkokin Waje A majalisar tarayyar turai ya maida wa zababben shugaban kasar Amurka martani.
Shugaban Kwamitin Harkokin Waje a majalisar tarayyar turai ya maida wa zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump martani akan sukar da ya yi musu.
Dan siyasar kasar Jamus, Elmar Brok wanda kuma shi ne shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar tarayyar turai, ya ce; maganar da Trump ya yi na cewa; An kirkiro tarayyar turai ne domin cutar da turai, ba wani abu ba ne ya sa shi fadin hakan sai hauka da rashin sanin tarihi.
Traump da jaridar Times ta yi hira a shi, ya yi suka akan siyasar karbar ‘yan gudun hijira da da kuma cewa; yin hakan babban bala’i ne.! Har ila yau Trump ya soki kungiyar yarjejeniyar tsaro ta NAto wacce ya ce; ta rube, don haka kasashen turai su ke son ficewa daga cikinta.
Shugaban kasar Faransa Fransua Hollande ma dai ya maida martani akan Trump da ya yi su ka akan tarayyar ta turai, tare da cewa; Basu bukatar wani daga waje, ya yi mana gyara.