An dai haifi Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’adu Abubakar ne a ranar 24 ga watan Augustan shekarar 1956 a birnin Sokoto dake Arewacin Nijeriya, kuma shi ne Sultan na 20 a ƙarƙashin Daular Usmaniya.
A matsayinsa na Sarkin Musulmi shi ne jagoran al’uman Musulmi miliyan fiye da 70 dake Nijeriya.
A ranar 2 ga watan Nuwanba ne dai Alhaji Sa’adu Abubakar ya gaji wansa marigayi Mohammadu Macciɗo Sultan na 19 wanda kuma ya rasu sakamakon wani hatsarin jirgin saman kanfanin ADC jim kaɗan bayan tashin sa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Sa’adu Abubakar shi ma ya kasance ɗa ga Sultan na 17, Saddiq Abubakar Usumanu wanda ya shafe shekaru fiye da hamsin akan karagar mulki.
Sultan Sa’adu ya shiga aikin Soji a shekarar 1975, kuma bayan ya kammala horon Sojin ne ya zama laftana wato mai anini ɗaya.
Bayan wannan kuma Sarkin Musulmin ya halarci kwasa-kwasai a ciki da wajen Nijeriya a ƙasashe da suka haɗa da Indiya da Kanada.
Bayan komowarsa gida ya zama kwamandan Sojojin Tankan Soji masu bada kariya ga shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1980.
Bayan wannan kuma ya zama kwamandan dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar OAU a Chadi.
Har ila yau Sarkin Musulmin ya zama wakilin Soji na Nijeriya a ƙungiyar Ecowas, bayan zama wakili a rundunar Sojin yammacin Afrika dake aikin wanzar da zaman lafiya a Saliyo.
Kafin naɗa shi Sarkin Musulmi na 20, Sa’adu Abubakar ya zama wakilin Sojin Nijeriya a ofishin Jakadancin Nijeriya a Pakistan.
Kuma yanzu haka yana da matar aure da kuma ‘ya’ya.