Taron CanJin Yanayi Na Duniya: Za’ayi Tsananin Zafi A Bana


Shekara ta 2016 za ta kasance shekara mafi zafi a duniya tun lokacin da aka fara adana bayanai kan yanayi, kamar yadda hukumar kula da yanayi ta duniya ta sanar.
Hukumar kula da yanayi ta duniya ce ta ba da sanarwar a wajen wani taron duniya kan yanayi da ake yi a Morocco. Wakilai a wajen taron na duba yadda zaben Donald Trump a matsayin shugaban Amurka zai shafi yarjejeniya kan dumamar yanayin duniya da aka cimma a Paris a bara.
Sai dai kuma wakilin Amurka na musamman a wajen taron, Jonathan Pershing, ya ce Amurka za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar Paris din, duk da sauyin gwamnatin da aka samu.
Mr Trump ya taba bayyana sauyin yanayi a matsayin wani abu da babu gaskiya a cikinsa, wanda China ta kirkira domin lalata masana’antun Amurka.

You may also like