Taron koli na Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DWBatun yakin Ukraine da Rasha da ya raba kan duniya, ya kasance babban batun da zai mamaye taron Majalisar Dinkin Duniya da aka bude a wannan Talata a birnin New York na kasar Amirka. Baya ga yakin Ukraine da ya janyo karancin abinci a duniya, kokarin kawo karshen fitar da hayaki mai gurbata iska da koma bayan Ilimi da barazanar da yunwa ke yi wa rayuwar mutum fiye da miliyan hamsin a yanzu, sun kasance cikin muhinman batutuwan da aka soma tafka mahawara a kansu a taron.

Shekaru biyu kenan, rabon da shugabanin su hadu wuri guda a sakamakon annobar corona inda aka koma gudanar da taron ta bidiyo, wannan ya sa majalisar, ta shawarci duk wani shugaban da ke da niyyar jawabi a zauren taron, da ya kokarta ya zo da kansa a maimakon bada jawabi ta bidiyo. Taron shi ne karo na 77 a tarihin majalisar.

      
 You may also like