Taron ministocin EU kan Turkiyya bayan yunkurin juyin mulki


Ministocin harkokin wajen kasashen EU na shirin gudanar da taro a wannan Litinin a birnin Brussels dan tattaunawa kan batutuwan da suka hada da halin da ake ciki a Turkiyya biyo bayan juyin mulkin da ya ci tura.

A lokacin wannan taro wanda zai samu halartar sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, ministocin harkokin wajen kasashen na kungiyar Tarayyar Turai za su yi kira ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya da ya kiyaye dokoki da kuma hakin dan Adam wajen daukar matakan kalubalantar wadanda suke da hannu a cikin yinkurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

Ko baya ga batun Turkiyya taron wanda a karo na farko zai samu halartar sabon ministan harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson zai tattauna kan batun yaki da ta’addanci da rikicin kasar Libya da na Ukraine da batun ‘yan gudun hijira daga kasashen Afirka.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like