‘Yan sanda a Zimbabwe sun tarwatsa wata zanga-zangar da masu adawa da shugabancin Robert Mugabe suka gudanar yau laraba a birnin Harare.
‘Yan sanda sun yi amfani da motocin ruwan zafi, kulake da kuma hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa daruruwan ‘yan adawar da suka taru a gaban ginin ma’aikatar kudin kasar.
A shekara ta 2009 ne gwamnatin kasar Zimbabwe ta dauki matakin daina amfani da takardar kudinta saboda matsalar hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar kudin inda ta dogara kan dala.
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe mai shekaru 92 wanda ke rike madafun ikon kasar tun bayan samun ‘yancinta daga Birtaniya a 1980 na fuskantar matsin lamba daga ‘yan adawar kasar na ya sauka daga mukaminsa.