Tarzoman Adawa Da Gwamnati: Osinbajo Ya Ankarar Da Kungiyoyin Kwadago



A yau Alhamis ne, Mukaddashin Shugaban Kasa, Femi Osinbajo ya ankarar da kungiyoyin Kwadago da ke zanga zangar adawa da halin da kasa ke ciki inda ya nuna masu babu yadda za a samu nasara ba ba tare da sadaukarwa.
Da yake jawabi ga mahalarta zanga zangar a fadarsa, Osinbajo ya nuna masu cewa gwamnati za ta  tuntubi kungiyoyin Kwadago da na masu zaman kansa game da shirin gwamnati kan yadda za a farfado da tattalin arzikin kasar nan wanda za a kaddamar a cikin wannan watan.

You may also like