Tarzomar Kiyayyar Sabon Shugaban Amurka na Yaduwa a Duniya Daruruwan mata a Nairobi babban birnin kasar Kenya sun hallara don shiga zanga-zangar kyamar shugaban Amurka Donald Trump.
Matan da suka hada da Amurkawa da ‘yan kasar ta Kenya, sun bi sahun macin mata miliyan dari a birnin Washington na Amurka, domin nuna adawa da ra’ayin Shugaba Trump na rashin ganin kimar mata.
Kungiyoyin kare hakkin mata sun hallara a birnin Washington don shiga sahun zanga-zangar nuna kyamar shugaba Trump din. Mutane dubu-dari-biyu ne ake sa ran za su yi gangami da maci a birnin na Washington.
Masu zanga-zangar sun ce za su yi macin ne don nuna jajircewarsu, kan adawar da suke yi da nuna wariyar jinsi, da rashin mutunta mata da Mr Trump ke yi.

Matan dai sun bayyana cewa Donald Trump na tutiya da cin zarafin mata ta hanyar lalata, da yawan zolaya ga mata game da surar da Allah ya musu.
Matan na fargabar mutunci da kuma matsayinsu zai ja baya a karkashin sabuwar gwamnatin Repulican. Zanga-zanga mafi girma kawo yanzu ita ce wadda ke gudana a birnin Sidney na Australia, inda kimanin mutane 3000 suka yi maci zuwa ofishin jakadancin Amurka suna caccakar Mr. Trump kan nuna halayyar raina mata.

You may also like