Majiyar rundunar ‘yan sanda a Somaliya ta sanar da cewa: Tashin wani bom a birnin Magadisho fadar mulkin kasar ya lashe rayukan mutane masu yawa.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto daga majiyar rundunar ‘yan sandan Somaliya cewa: Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da wani ginin otel a birnin Magadisho fadar mulkin kasar a safiyar yau Laraba, lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 12 tare da jikkatan wasu kimanin 25 na daban.
Rahotonni sun bayyana cewa: A bayan tashin bom din wasu gungun ‘yan bindiga sun kutsa cikin otel din da nufin yin garkuwa da mutane, amma har yanzu babu cikakken bayani kan halin da ake ciki.