Tashin hankali na kassara ilimin yara


Ranar takwas ga watan Satumba rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin ranar yaki da jahilci da yin duba kan nasarori ko akasin haka da aka samu a kokarin yaki da jahilci a fadin duniya.

Nigeria Makoko schwimmende Schule in LagosBisa al’ada dai kamata ya yi a ga yara sun je makaranta cikin annashuwa dan samun ilimi

Bikin wannan shekara dai wanda na shekaru 50 ne, na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin farfado da harkokin ilimi a shiyyar Arewa maso Gabas a Najeriya, bayan da rikicin Boko Haram ya dakatar harkokin ilimi a sassan shiyar. A iya cewa dai babban miki da rikicin Boko Haram ya haifar a shiyar Arewa maso Gabas na Najeriyar, shi ne na gurgunta harkokin bunkasa ilimi musamman na Boko wanda kungiyar da ke gwagwarmayar ta haramta shi.

Nigeria Boko Haram Angriff in Gamboru Makarantu sun koma kufayi saboda ta’addancin Boko Haram

Baya ga hare-hare da aka kai makarantu tare da hallaka dalibai da kuma sace wasu daliban musamman mata, an rufe makarantu da dama a jihohin Borno da Yobe da Adamawa saboda sauke dubban ‘yan gudun hijira a cikinsu. Wannan ba karamin koma baya ya haifar ba a harkokin ilimi a shiyar Arewa maso Gabas din a Najeriyar, yankin da dama ya kasance mafi koma baya a bunkasar ilimi tsakanin takwarorinsa na kasar. Iyaye da yara da masu ruwa da tsaki na ci gaba da bayyana damuwa kan rashin zuwan yaran makaranta musamman a jihar Borno, inda wani bawan Allah a Maiduguri ya ce rashin zuwan ‘ya‘yansa makaranta ya jefa su cikin wani hali.

Oberschüler in Tahoua, NigerWasu dalibai dai kan daure zuwa makaranta

Yanzu haka dai Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar ya fito da shirin daukar nauyin karatun yara marayu, a inda yanzu ake shirin daukar yara kusan 2.000 a Gombe da Kwami bayan sama da 1.000 da ya dauka a shekarar karatun bara, abin da ake ganin zai taimaka gaya wajen habaka harkokin ilimin a shiyar ta Arewa maso Gabas a Najeriyar.

You may also like