Tattalin arzikin Najeriya ya karye


Wasu alkalumman Hukumar Kididdiga a Najeriya sun nuna tattalin arzikin kasar ya koma baya sosai fiye da yadda aka samu a shekarun baya.

Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, ta fidda wasu alkalumma da ke nuna cewar tattalin arzikin kasar na fuskantar barazana. Alkalumman na nuni da cewa tattalin arzikin kasar ya sauka da kusan kashi biyu cikin dari a kasa da watanni uku da suka gabata.

 

0,,18350541_303,00

 

Alkalumman sun bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da Najeriya ta fada matsin tattalin arziki mafi muni cikin shekaru 10 da suka shude, wanda a yanzu ya jefa ‘yan kasar cikin halin matsi na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi.

Sai dai kuma alkalumman sun nuna cewa komadar ta wannan lokacin ba ta kai ta watanni ukun farko na mulkin shugaba Muhammadu Buhari ba. Najeriya dai na cikin jerin kasashen da ke kan gaba wajen albarkatun man fetur a nahiyar Afirka baki daya, to amma ta dogara ne kacokan bisa kudaden da ake samu daga sayar da man.

You may also like