
Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron raga, David de Gea ya ce tattaunawa da yake da Manchester United kan batun tsawaita kwantiraginsa za ta zama alheri.
Yarjejeniyar golan mai shekara 32 da United za ta kare a karshen kakar bana, wanda ya yi wasa 517 a kaka 12 kawo yanzu.
A wannan lokacin yana da damar tuntunbar wasu kungiyoyin da zai iya komawa da taka leda idan yana bukatar hakan.
”Har yanzu ina tattaunawa da United, in ji De Gea. ”Ina da tabbacin cewar sakamakon zai samar da labari mai faranta zuciya.”
United ta doke Crystal Palace 2-1 a Old Trafford a wasan mako na 22 a Premier League ranar Asabar.
Da wannan sakamakon kungiyar Old Trafford tana ta uku a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki takwas tsakaninta da Arsenal mai jan ragama.
Kenan United ta yi karawa 13 a gida a jere a dukkan fafatawa ba tare da an doke ta ba.
Kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama za ta buga wasan karshe da Newcastle United a Carabao Cup ranar 26 ga watan Fabrairu a Wembley.