Tattaunawar Sulhu Tsakanin Fulani Makiyaya Da Manoma Ta Yi Nasara A Kasar Ibo


 

A jiya Juma’a ne aka gabatar da wani muhimmin zama don tattauna wata matsala da ta ke ci wa bangarori biyu (fulani makiya da manoma a daya a bangaren) da suka kasance masu muhimmanci ga tattalin arzikin Nijeriya tuwo a kwarya don kawo karshen wutar gabar da jima tana ci a tsakaninsu.

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen Kudu Maso gabashin Nijeriya ne suka shirya wannan batu na tattaunawa a matsayin wani bangare na raya makonta da ta kammala a jiya Juma’ar.

Taron da aka gudanar a Enugu, babban birnin jihar ta Enugu ya tara shugabancin kungiyar Miyetti Allah ta kasa baki daya da ma shugabancin Miyetti Allan na jihohi 36 har da Abuja, abinda sakataren kungiyar Miyetti Allah ta kasa ya bayyana cewa ba a taba samun hakan ba.

Haka kuma kungiyoyin sa kai da shuwagabannin al’umma da masu ruwa da tsaki daga bangarorin kudu da arewacin Nijeriya sun halacci wannan zama na tattauna batun sulhu a jiya inda aka gabatar da kasidu da bayanan illolin da rashin jituwar makiyaya da monoma ke haifarwa tar da bayanin hanyoyin da za a bi don kaucewa afkuwar illolin a gaba da kuma bayanin jaddada zaman lafiya, hadin kai tare da dawo da zumuncin da tun da da akwai shi wanda rashin fahimta ya sanya ya yi tsami

Abinda ya fi jan hankali a wannan taron shi ne kasidar da babban bako mai jawabi, Mejo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya gabatar mai taken: Matsalolin Makiyaya a Nijeriya: Mene ne Mafita?

Mejo Hamza Al-Mustapha ya yi bayani na kurakuren da ake samu daga bangarorin makiyaya da suka hada da barin yara kanana da ba za su iya gudanar da dabbobi yadda ya kamata ba kiwo ta yadda sai dabbobin su fada gonaki kuma yaran su kasa shawo kansu da wuri da kuma fita kiwo da daddare da kuma barin hanyoyin da aka tanada don kiwo zuwa gonaki da dai sauransu

Daga daya bangaren kuma, Mejo Al-Mustapha ya bayyana cewa manoma a kokarinsu na fadada abinda suke nomawa sun wawashe hanyoyin kiwo da gwamnatoci suka tanadawa fulani makiyaya don kiwo. Haka kuma manoma sun fadada gonakinsu har gab da titi ta yadda babu yadda makiyayi zai yi a lokacin da ya ke kokarin yin hijiri ko kora dabbobinsa zuwa kiwo, sai dai ya bi kan titi ko kuma ya shiga gona

Har ila yau, Mejo Hamza ya bayyana cewa kashe-kashe musamman da bindigu da ake bayyana makiya na aikatawa akan manoma da kuma ‘yan na gaji gari akwai al’ummara na siyasa da wasu wadanda ke ribatar rashin zaman lafiya a Nijeriya ke yi.

Mejo Hamza ya yi bayanin hanoyin da za a samar da mafita ta din-din-din daga wannan matsala ta hanyar samar da kungiyoyi masu rai na manoma da makiya a kowane loko da sakon kasar nan kuma a karkashin inuwar uwar kungiya daya.

Mejo ya ci gaba da cewa ya zama dole kowane makiyayi ya kasance yana da takardar shaida ta yadda hakan zai zame masa lasisin gudanar da sana’arsa ta kiwo a duk lokacin da jami’an tsaro suka bukaci da ya bayyana kansa. Ta wannan hanya ne za a iya tantance makiyaya ‘yan asalin kasar Nijeriya da kuma wadanda ke shigowa daga wasu kasashen su zo su gudanar da ta’addanci a matsayin fulani makiyaya namu na gida Nijeriya.

Mejo Hamza ya yi jan hankali ga hukumomin tsaro da sanya idanu kan yadda makamai ke shiga da fita a adin kasar da ma wadanda ke safara da ajiyarsu da kuma da wace iriyar manufa ake saya da ajiye makaman?

Anan Mejo Hamza ya baiwa ‘yan siyasa laifin yawaitar makamai a hannun ‘yan ta’adda da matasa marasa aiki wadanda sau tari su ke zama barayin shanu, ko ‘yan fashi da makami ko masu garkuwa da mutane da dai sauransu.

A jimlace dai Mejo Hamza Al-Mustapha a kasidar ya ta’allaka mafi girman laifi ga gwamnati da hukumomin tsaro bisa yadda suke shakulatan bangaro da batun rikicin fulani makiyaya da manoma a kasar, wanda a cewarsa shi ya kai ga rikicin kai wa kololuwar da ya kai

Bayan bayanai da bangarorin masu ruwa da tsaki suka gabatar kan yadda za a shawo kan matsalar, kungiyar Miyetti Allah ta kasa baki daya ta hannun shugabanta na kasa baki daya, Alhaji Kiruwa Zuru ya mika takardar sulhu da kiyaye wasu sharudda ga kafatanin manoma da mazauna kudu maso gabashin Nijeriya ta hannun Mukaddashin shugaban kungiyar ‘yan kabilar Ibo ta Ohaneze Ndigbo ta kasa da kasa baki daya, Cif O.A.U Onyema.

An kammala taron sulhun cikin aminci da karin fuskantar juna.

Wasu muhimman mutane da kungiyoyi a wajen wannan taro sun hada da:

Gwamnan jihar Enugu, Rayit Honarabul Ifeanyi Ugwuanyi

Tsohon Ministan yada labarai na Nijeriya wanda shi ne shugaban taron, Cif John Nnia Nwodo

Mejo Hamza Al-Mustapha mai ritaya wanda ya kasance bako mai jawabi

Cif O.A.U Onyema-mukaddashin shugaban Ohaneze Ndigbo ta kasa da kasa

Kwamared Christopher Isiguzo, mataimakin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen C da ke kudo maso gabashin Nijeriya

Rex Chinweuba Arum, Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Enugu

Sarkin yankin Egede Udi, Igwe Polycarp Ifeanyichukwu Oyigbo

Sarkin Hausawa jihar Enugu, Alhaji Yusuf Abubakar Sambo II

Kungiyar Vibrant Green Youth Development Initiative a karkashin jagorancin Dakta Olokun Mustapha

Kungiyar Lauyoyi Matasa Ta Arewacin Nijeriya a karkashin jagorancin Abubakar Sadik Ilelah

You may also like