Tawagar yan gudun hijira zata fafata a gasar Olympics


 

Wasu daga cikin yan gudun hijira masu wasannin motsa jiki daga kasar Sudan ta Kudu sun bayyana jin dadi game da damar da aka basu ta fafatawa a gasar Olmpics da za a yi a birinin Rio na kasar Brazil.

A gasar da zata gudana a wannan shekara akwai tawagar masu tsalle tsalle da guje-guje dake wakiltar kafatanin masu gudun hijira na kasashen duniya.

Ita dai wannan tawagar ta masu motsa kiji da ke wakiltar yan gudun hijirar ta kunshi maza 6 da kuma mata hudu, biyar daga kasar Sudan ta Kudu, biyu daga kasar Syria, sai kuma sauran biyun daga jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo, yayin daya kuma dan kasar Ethiopia.

Kuma da yawa daga cikinsu sun kwashe tsawon shekaru 10 suna gudun hijira bayan tserewa daga kasar Sudan a waccan lokaci kenan saboda rikicin da kasar ta yi fama dashi na ballewar yankin Sudan ta Kudu.

Wasannin da masu wakiltar yan gudun hijirar a gasar Olympics din zasu taka rawa sun hadar da Linkaya, Judo, sai kuma wasu wasanni na tsalle tsalle.

Daya daga cikin yan wasan James Chiengjiek dan kasar sudan ta kudu, ya ce wannan dama ce garesu ta nuna cewa masu gudun hijira fa ba kanwar lasa bane a fagen wasanni.

In ba-a manta ba dai za-a fara gasar ta Olympics 5 ga watan Agusta zuwa 21 ga watan kuma wannan shine karo na farko da aka samar da wata tawaga da zata fafata a gasar da ta kunshi yan gudun hijira zalla.

You may also like