Taylor ne zai busa wasan Real da Al Hilal a Club World Cup



Anthony Taylor

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta sanar da nada Anthony Taylor, wanda zai hura wasan karshe a Club World Cup a Morocco ranar Asabar.

Alkain gasar Premier zai gabatar da aikin tare da mataimaka Gary Beswick da kuma Adam Nunn dukkan su daga Ingila.

Ranar Asabar za a buga wasan karshe a gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi tsakanin Real Madrid da Al Hilal ta Saudi Arabia.

Real Madrid ce mai kofin zakarun Turai Champions League, ita kuwa Al Hilal ita ce ta lashe na zakarun Asia.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like