
Asalin hoton, Getty Images
Ranar Asabar Manchester United za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan Premier League a Old Trafford.
Kungiyoyin sun tashi 1-1 a Selhurst Park a wasan farko a Premier League a bana ranar 18 ga watan Janairu.
United tana ta hudu a kan teburin Premier da maki 39, iri daya da na Newcastle United, wadda take ta uku.
Ita kuwa Palace mai maki 24 tana ta 12 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
Kawo yanzu ana ganin cin gaban da United ke samu karkashin Erik ten Hag, wanda ya karbi aiki a bana daga Ajax.
United ce kadai take takarar kofi hudu a bana a Ingila, wadda tuni ta kai wasan karshe a Carabao Cup a Wembley da za ta fafata 26 ga watan Fabariru.
Haka kuma kungiyar tana cikin takarar lashe FA Cup da Premier League da Europa Cup, wadda za ta fuskanci Barcelona.
United ta yi wasa takwas ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba a Premier League a kakar nan, iri bajintar da ta yi kenan a bara.
Idan har United ta yi nasara a kan Palace zai zama nasara ta shida kenan a Old Trafford a jere a karon farko.
Kungiyar ta ci wasa takwas a jere a Premier League tsakanin Mayu zuwa Nuwambar 2017 karkashin Jose Mourinho.
Maki 39 da Ten Hag ya hada bayan wasa 20 a Premier ya yi kan-kan-kan da kwazon Jose Mourinho a kakar farko a horar da kungiyar Old Trafford.
Ole Gunnar Solskjaer ne ya sha gaban Ten Hag mai maki 40 a wasa 20 da fara jan ragamar United.
United ta lashe wasa 12 a jere a gida a bana a dukkan fafatawa, tun bayan 0-0 da Newcastle United a Premier League ranar 16 ga watan Oktoba.
A karkashin Sir Alex Ferguson ne United ta yi wasa 20 a gida a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa.