
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta gabatar da kunshin kwantiragin kaka uku ga Erik ten Hag, domin ya ci gaba da horar da kungiyar, duk da batun da ake na kokarin sayar da ita. (Mirror)
Chelsea na son daukar golan, Leeds United, Illan Meslier, mai shekara 23 a karshen kakar nan. (Football Insider)
Newcastle United za ta sake zawarcin daukar dan kwallon Bayer Leverkusen, Moussa Diaby, mai shekara 23 da kuma Mitchel Bakker, mai shekara 22. (90min – in German)
Dan wasan da Arsenal ta dade da son saya, Diaby, Newcastle United ma na bukatar dan wasan da aka ce darajarsa za ta kai fam miliyan 62. (Express)
Wakilin Mohamed Salah, Ramy Abbas Issa ya yi watsi da batun da ake cewar dan wasan na son barin Liverpool. (90min)
Asalin hoton, Getty Images
Roberto Firmino, mai shekara 31, na son ya ci gaba da taka leda a Turai, idan ya bar Liverpool a karshen kakar bana. (Football Insider)
Liverpool da Manchester United na son daukar dan kwallon Anderlecht, mai tsaron raga, Bart Verbruggen, mai shekara 20. (Het Laatste Nieuws – in Dutch)
Dan kwallon Ghana, Mohammed Kudos ya mayar da hankali kan yadda Ajax za ta kare kofin gasar Netherlands da take da shi na bara, maimakon rade-radin da ake zai koma Manchester United, ya ce zai tsawaita yarjejeniyar a Ajax idan lokacin ya yi. (De Telegraaf – in Dutch)
Tottenham na bibiyar dan wasan Watford, Adrian Blake, mai shekara 17, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar bana, dan kwallon tawagar Ingila ya fara kungiyar tun yana da shekara tara da haihuwa, amma har yanzu bai fara buga mata lik ba. (Mail)
Borussia Monchengladbach za ta hakura da Manu Kone ya bar kungiyar, wanda Chelsea da sauran kungiyoyi ke son sayen dan wasan mai shekara 21 dan kasar Faransa. (Caught Offside)
Watakila tsohon dan wasan tawagar Faransa da Arsenal Patrick Vieira da Thierry Henry su yi zawarcin aikin horar da tawagar kwallon kafar Amurka. (Goal)
RB Leipzig na sa ran mai tsaron baya, Josko Gvardiol zai so komawa Real Madrid, maimakon buga gasar Premier League, amma ba a tabbaci ko Real za ta sayi dan wasan mai shekara 21 da ake cewar kudinsa ya kai fam miliyan 100. (90mins – in German)
Paris St-Germain a shirye take ta biya Napoli £159m, domin ta dauki dan kwallon Georgia, Khvicha Kvaratskhelia, 22. (Corriere dello Sport – in Italian)